Shugaba Bola Tinubu na ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a fadarsa da ke Aso Rock Villa, Abuja.
Jaridar PUNCH ta fakaito ayarin motocin Akpabio sun yi jerin gwano a wajen harabar majalisar da yammacin Laraba.
- Juyin-juya-halin Kyautata Muhalli: Rawar Da Kasar Sin Ke Takawa Wajen Samar Da Makoma Mai Kyau
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Dattijon Kasa, Edwin Clark
An kuma hangi wasu motoci na shiga cikin Villa amma ba a iya tantance mutanen da ke cikin motocin ba kuma lamarin ya ci tura ga ‘yan jarida gano wadanda ke cikin motocin.
Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.
Da yake jawabi a zaman taron na ranar Laraba, Akpabio ya ce Nijeriya ba za ta bar Hukumar USAID ta ci gaba da aiki a Nijeriya ba idan aka same ta da laifin daukar nauyin ta’addanci.
Ya ci gaba da cewa, yana da muhimmanci Nijeriya ta tabbatar da gaskiyar wannan zargi.