Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana damuwarsa kan yadda malaman addini ke ci gaba da shiga harkokin siyasa, inda ya bayyana cewa malaman addini a yanzu suna da tasirin gaske kan masu zabe da kuma harkokin siyasa.
Lamido ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da aka watsa a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna sakamakon rasuwar babban dansa.
- Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II
- Duk Wanda Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani, Shi Ma Sai An Hukunta Shi – Gwamna Sule
Tsohon gwamnan Jigawan ya koka da yadda malaman addini suka mamaye fagen siyasa, inda suka fito karara suna kamfen ga ‘yan takara tare da jagorantar mabiyansu kan wadanda za su mara wa baya.
“Duk da albarkar da malaman addini suke da ita, amma a yanzu malaman addini suna kokawar neman mulki. Ya kamata malamai su zama masu kulawa da ’yan siyasa, amma tun da suna son mulki, mu ’yan siyasa mun yanke shawarar komawa gefe mu zuba ido. Muna jiran su fada mana wanda za mu zaba bisa ga burinsu. Domin samun daidaito da adalci, ya kamata kowa ya kiyaye matsayinsa a cikin al’umma,” in ji shi.
Lamido ya bayyana cewa, kamar yadda jam’iyyun siyasa ke fama da rikicin cikin gida, su ma kungiyoyin addini na fuskantar rarrabuwar kawuna, inda ya yi gargadin cewa yanayin siyasar Nijeriya zai kasance cikin rudani matukar ba a samu hadin kai ba.
Idan za a iya tunawa dai, malaman addini sun taka rawa wajen zaburar da jama’arsu domin yin rajistar masu zabe. Duk da haka, a babban zaben 2023 wanda yana daya daga cikin mafi zaben da ya janyo rarrabuwar kawuna a Nijeriya, masallatai da coci-coci sun taka rawar gani wajen tursasa mabiyansu su zabi nasu ‘yan takara.
Mafi yawancin wa’azi da khudubobi sun kasance wurin tattauna harkokin siyasa. A wasu majami’u, fastoci sun yi da’awar manzancin kan ‘yan takararsu, yayin da a cikin malaman addinin musulmi, limamai sun bukaci mabiya da su yi zabe ta hanyar addini. Abin mamaki, yawancin wadannan hasashen addini ba su tabbata ba.
A kwann nan dai an tafka cece-kuce kan taron da aka shirya gudanarwa a ranar 22 ga watan Fabrairun 2025 a Abuja, wanda ake sa ran za a hada mahardata alkur’ani har 30,000. An dage taron ne ba tare da saka wani lokaci ba, sakamakon kalubalantar lamarin da wasu malaman addinin Islama suka nuna, inda suka nuna shakku kan sahihancinsa tare da zargin cewa wani yunkuri ne na siyasa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Idn za a iya tunawa dai, tikitin tsayawa takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na Musulmi-musulmi a shekarar 2023, wanda kusan ya wargaje tsarin fagen siyasa, a karshe ya tsira saboda gagarumin goyon baya daga malaman addini da suka tabbatar wa mabiyansu. Shi ma kabilanci da bangarenci, musamman a kudu maso yamma ya taka rawar gani.
A lokacin zaben 2023, abokan Tinubu a arewacin Nijeriya sun yi zawarcin manyan malaman ddinin Musulunci, inda suka samu goyon bayansu. Yanzu, da alama ana ci gaba da yin irin wannan kokarin, yayin da ‘yan wasan siyasa suka fara dabarun lashe zabe a 2027.
A daya hannun kuma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ana kyautata zaton zai sake dauko abokin takararsa daga yankin arewacin kasar da galibinsu musulmai ne a zabe mai zuwa. Kasancewarsa yana halartar tarukan da suka shafi addinin Musulunci, ana kallonsa a matsayin wanda yake kokari wajen jawo hankalin malaman addini domin samun nasara.
Magoya bayan Obi sun ce baya ga zargin tafka magudin zaben da kuma gazawarsa wajen shigar da shugabannin addini a arewacin kasar ya taimaka matuka gaya wajen rashin nasararsa a 2023. Yayin da zaben 2027 ke gabatowa, da alama magoya bayansa sun kudiri aniyar kauce wa kuskuren da suka yi a zaben da ya gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp