Ɗaya daga cikin wadanda suka yi hadakar mallakar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Sir Jim Ratcliffe na duba yiwuyar yadda za a kara rage ma’aikatan kungiyar. Wata majiya ta tabbar da cewar Manchester United na duba yadda za ta sake rage kudin da take kashewa da zai kai £300m a shekara uku wanda hakan ne zai taimaka wajen samun kudin sayen ‘yan wasa.
United ba ta ce komai ba kan rahoton cewar Ineos Group, karkashin jagorancin Sir Jim Ratcliffe na auna yadda zai sake rage ma’aikata kimanin 100 zuwa 200 ba. Daga baya ne za a fayyace yawan ma’aikatan da za a rage da guraben da suke aiki, domin aiwatar da shirin. Haka kuma
- Harry Maguire Ya Sanya Hannun Kwantaragin Shekara Ɗaya A Manchester United
- Me Kuka Sani Dangane Da Wasan Hamayya Tsakanin Ac Milan Da Inter Milan?
United za ta rufe ofishinta da ke Landan a Kensington, amma ta sanar cewar za ta ci gaba da kasancewa a cikin birnin don huldar kasuwa.
Tun farko United ta rage ma’aikata 250 da cire butum butumin Sir Aled Ferguson a matakin jakadan da ake biya da soke biyan kudi ga ma’aikata, domin zuwa kallon wasan karshe. United ta ce za ta yi amfani da kudin da za ta samu daga rage ma’aikatan, wajen bunkasa babbar kungiyar da sauran ayyukan da suke bukatar a kashe musu kudi domin a inganta su yadda ya kamata.
Ƙungiyar ta ce kudin da za ta samu zai kai £45m a kowacce shekara daga rage ma’aikatan, sannan kuma wani babban jami’in kungiyar da ya dade kan mukamin kula da gudanar da United, Jackie Kay wanda yake Old Trafford shekara 30 zai ajiye aikinsa duka a cikin sauye-sauyen da kungiyar take yi na rage ma’aikata domin rage kashe kudin da ake yi kusan duk shekara.
Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai fam miliyan (£300m) a United, domin bunkasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon filin wasa sannan ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe sama da fam biliyan biyu (£2bn), ko kuma a yi wa tsohon filin wasa na Old Trafford kwaskwarima da zai ci Fam biliyan 1.5.
Manchester United ta sanar da yin hasarar kasuwanci da ya kai Fam miliyan 113.2 daga ranar 30 ga watan Yunin 2024 kuma kawo yanzu kungiyar tana mataki na 15 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 24. Amma kuma har yanzu kungiyar tana buga gasar cin kofin Europa Leage da gasar cin kofin kalubale na FA Cup da kungiyar za ta fafata da Fulham a farkon watan gobe.