Wasa tsakanin Ac Milan da Inter Milan na daya daga cikin wasannin kwallon kafa da ke matukar daukar hankalin masu sha’awar kwallon wasannin a fadin Duniya duba da irin tarihi da tasirin da ke tattare da wasan.
‘Derby della Madonnina’ wasa ne wanda ake buga shi tsakanin kungiyoyi guda 2, da su ke kasa daya, jiha daya, gari daya, unguwa daya da kuma filin wasa daya, wato – Ac Milan da Inter Milan.
Takaitaccen tarihin Derby della Madonnina
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.
Wanda yafi yawan jefa kwallaye:
Andriy Shevchenko kwallaye 14.
Nasara mafi girma:
inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).
Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina
Paolo Maldini wasanni 56.
Haduwar da akafi jefa kwallaye
Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).
Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda
José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).
Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan
Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).
Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu sun hadu da juna sau 224 a dukkan gasar da suka buga inda Inter Milan ke gaba a wajen samun nasara yayin da ta doke abokiyar karawarta sau 85 akayi canjaras 66 sannan Ac Milan ta samu nasara sau 73.