Duk da yake dai labarai na Baka da aka samu dangane da Keita ya nuna bai taba barin addinin gargajiya ba. Irin wadancan labarin na fatar Baki sun nuna cewa Sundiata Keita shi matsafi ne wanda kuma ya amince da addinin gargajiya na Malinke. Amma wasu majiyoyin labarai masu yawa sun nuna cewa ya ce Musulmai su yi aiki da Musulmai wadanda su ‘yan kasuwa ne, shi kuma mai bin addinin gargajiya ne na Malinke ya umarci mutanensa su yi aiki tare da sauran mutanen.
Koma dai menene ko ma ace s shi mai bin addinin Malinke ne sau da kafa, ko kuma shi kuma Musulmi ne ko kuma yanea yin duka addinan guda biyu, sai dai kuma babu wani tahakikanin abinda wani zai iya cewa dangane lamarin addinin da yake amma shi ya iya salon tafiyar da mulki,sai dai kash! Sha’anin abinda ya shafi ko wane irin addini ya fi ba muhimmanci wannan magana ba wanda zai iya cewa wani abu dangane da hakan.
- Ciwon Daji: Adadin Masu Warkewa A Nijeriya Ya Yi Kaɗan – Pink Africa
- Mummunan Hatsari Ya Kashe Mutane 23, Da Yawa Sun Jikkata A Kano
Keita ya mutu a shekarar 1255 daga cutar da ba za a iya yin wani bayani kan wacce iri ce ba, duk da yake wasu na cewa ya mutu ne ta hanyar hatsari.Mutumin da shi ne ya kafa Daular Mali, wanda ake ta yawan fadar maganganu babu dadi akan shi wanda kuma da Baka ne amma duk da haka nana yi ma shi kallon gwarzon mutum ne.Sai ga Daular da ya kafa ta kasance daya daga cikin kasashen da suke da arziki a duniya, wasu daga cikin mutanen da suke daga tsatson shi ko wani wanda yafi kowa arziki da ya taba rayuwa , Mansa Musa.Mulkin sa tare da taimakon soja sun bar Daular ta ci gaba da kasancewa wadda ta kai ganin har zuwa karni na 16, inda ake ta kara jinjina ma sa da Daular sa, iyalansa, inda abin har ya kai ga daurewa masu labarin Baka kai a fadin duniya kan lamarin na shi.
Mansa Mūsā na farko (I )Mali (ya mutu ne shekarar 1332 37) shi Mansa newa ( wato babban jarumi) na yammacin Afirka ita Daular Mali daga shekarar 1307 (ko kuma 1312).Mansa Mūsā ya bar wani abinda da ya yi saboda arzikin da ayek da shi wanda ya daurewa mutane kai— kwarai da gaske bayan da ya gina babban Masallacin Timbuktu— wanda hakan ce ta sa har yanzu ana tunawa da shi a gabas ta tsakiya,da kuma yammacin Turai saboda irin aikin Hajjin da ya tafi zuwa Makka a shekarar (1324).
Tafiyarsa zuwa aikin Hajji
Mansa Mūsā, ko dai shi jikan ko kuma abokin wasan Sundiata wanda shi ne ya kirkiro Daular Mali yah au kan karagar mulkin ne a shekarar. A karni na 17 (1324),lokacin ne ya tafi aikin Hajjin wanda ya zama abinmagana saboda dalilai masu dama. Aikin Hajjin da ya tafi ne ya sa idon duniya ya bude saboda irin arzikin da Allah ya yi wa kasar ta Mali.