Shugaban kungiyar mata manoma (AFAN) ta Jihar Kano, Hajiya Fatima Sharu Gambo Yako, na daya daga cikin ‘yar kwamitin shirya bikin baja kolin kayan abincin azumi da cibiyar ciniki da masana’antu ma’adanai da aikin gona (KACCIMA) ta shirya, domin saukaka wa al’umma a lokacin watan azumin Ramadana.
Sidiya ta ce wannan baje koli ya kunshi kayan amfanin gona kamar irinsu shinkafa, wake, dawa, masara, gyada, manja, man gyada, doya, kwai da sauran kayayyaki da masa’antu da kamfanoni suke sarrafawa.
- Jirgin Saman Da Kasar Sin Ta Kera Mai Amfani Da Lantarki Ya Yi Tashin Farko Cikin Nasara
- Gwamnatin Tarayya Da Kasar Faransa Sun Sake Sabunta Yarjeniyar Farfado Da Hakar Ma’adanai
Haka kuma ta yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan yadda ya dada sabon kwamishinan ciniki da masana’antu na Jihar Kano, Alhaji Wada Sagagi wanda yake da kyakyawar alaka da wannan cibiya da ‘yan kasuwar Kano baki daya da kuma yadda ya yi ruwa da tsaki wajen ganin wannan baja kolin ya samu nasara ta hanyar ganin al’umma ta samu saukin kayayyaki amfani da azumi.
Ta yi kira ga kamfanoni da manoma da ‘yan kasuwa da sauran al’umma su halarci wannan kasuwa domin baja kolin kayansu ko kuma samun kaya cikin sauki, wajen yin amfanin azumi a wannan wata na Ramadan.