Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci tare da zaman kungiyar ciniki ta duniya, watau WTO a matsayin wadda za ta yi uwa-ta-yi-makarbiya a kan tsarin, kuma za ta ci gaba da mara baya ga yin garambawul a kungiyar ta kasa da kasa.
Wang, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babbar darektar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen G20, a birnin Johannesburg, birni mafi girma kuma cibiyar hada-hadar tattalin arzikin Afirka ta Kudu.
A nata bangaren, Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, a tsakiyar rudanin da duniya ke fama da shi, kasar Sin ta hau kan turba mai kyau, da cimma burin rage talauci da MDD ta sanya a gaba tun kafin cikar wa’adin da aka sa, da bunkasa masana’antu cikin hanzari, da kuma samun nasarori a fannin ilimi, tana mai cewar, nasarar da kasar Sin ta samu ta zama abar koyi ga sauran kasashe masu tasowa.
Darektar ta kungiyar WTO ta yaba da kudurin kasar Sin na warware takaddamar ciniki ta hanyar yin shawarwari da tuntubar juna bisa tafarkin da ya hade sassa daban-daban cikin kaifin basira da nuna dattaku. Ta kuma ce, kungiyar ta WTO na fatan ci gaba da samun goyon baya mai karfi daga kasar Sin wajen inganta yin garambawul a cikinta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)