Babban hafsan Sojojin Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya nuna damuwa kan ƙarancin kuɗin abinci da ake bai wa Sojoji a kullum, wanda a halin yanzu ke kan N1,500.
Yayin da yake jawabi ga jami’ai da sojojin Rundunar 81 ta Sojojin Nijeriya a filin taro na 9th Brigade da ke Lagos, Janar Oluyede ya sanar da cewa nan da ƙarshen wata mai zuwa, za a ƙara wannan kuɗi zuwa N3,000 a rana.
Baya ga wannan ƙari, Janar Oluyede ya bayyana cewa Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙaddamar da shirin lamuni mai ragi na 3% domin tallafa wa Sojoji wajen aiwatar da ayyukan ci gaban kansu. Duk da haka, ya ja hankalin Sojojin da su nemi bashin ne kawai idan lallai suna buƙata, domin yana iya zama ƙalubale wajen biyan sa, ko da yake kuɗin ruwan kan bashin kaɗan a cewarsa.
- Gwamna Buni Ya Jaddada Bai Wa Sojoji Gudunmawar Kawo Karshen Boko Haram
- Kakakin Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ya Yi Fatali Da Zargin Australia A Kan Atisayen Sojojin Kasar
Dangane da matsalar gidaje, babban hafsan Sojojin ya amince cewa da yawan Warrant Officers suna fuskantar matsalar rashin mallakar gidajensu bayan ritaya. A sakamakon haka, ya ce rundunar ta faɗaɗa shirin samar da gidaje masu sauƙin kudi ga Sojoji a wurare daban-daban da suka haɗa da Abuja, Ibadan, Jos, Fatakwal, Owerri da Akwa Ibom.
Wannan mataki na ƙarin kuɗin abinci da tallafin bashi da kuma shirin gidaje yana daga cikin sauye-sauyen da rundunar ke yi domin inganta rayuwar Sojojin da ke aiki, tare da basu ƙwarin gwuiwa wajen gudanar da aiyukansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp