Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na shirin sake duba tsarin farashin wutar lantarki domin magance rashin daidaito a biyan kuɗin wuta da kuma ƙarfafa saka hannun jari a fannin.
Ya bayyana hakan ne a taron gabatar da sabon tsarin manufar wutar lantarki da shirin kula da albarkatun wuta na Nijeriya da aka gudanar a Abuja. A cewarsa, jinkirin sauya kwastomomin rukunin B zuwa B ya samo asali ne daga rashin jajircewar kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) wajen saka hannun jari.
- Jirgin Saman Da Kasar Sin Ta Kera Mai Amfani Da Lantarki Ya Yi Tashin Farko Cikin Nasara
- Katsewar Wutar Lantarki: Mun Yi Asarar Fiye Da Naira Biliyan 6 – KEDCO
A halin yanzu, kwastomomin rukunin B da ke samun wuta na tsawon awanni 17 zuwa 18 suna biyan N63 a kowanne kilowatt, yayin da masu rukunin A da ke samun ƙarin awa biyu kacal ke biyan N209 a kowanne kilowatt.
Ministan ya bayyana hakan a matsayin rashin adalci, inda ya ce dole ne a sake duba tsarin don tabbatar da daidaito. Ya kuma jaddada cewa ba wai gwamnati na shirin ƙara farashi bane, amma tana duba hanyoyin inganta tsarin don bai wa kowa haƙƙinsa.
Adelabu ya ce kamata ya yi kwastomomin da ke rukunin B da C su sami tsarin da bai cutar da su ba, domin haka gwamnati tana shirin rage giɓin farashin da ke tsakanin rukunin A da sauran rukunan. Ya ce matakin zai taimaka wajen ƙarfafa saka hannun jari a fannin wutar lantarki tare da gyara kayayyakin da suka lalace don samar da wuta mai ɗorewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp