Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau ranar 27 ga wannan wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da maida batun samun bunkasuwa a matsayin batu mafi muhimmanci a cikin ajendar kasa da kasa, da bin tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, da zama babbar kasa mai ba da muhimmiyar gudummawa a duniya, don tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.
Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin ta kiyaye sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya. A matsayin kasa ta biyu mafi ci gaban tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 cikin dari ga bunkasuwar duniya, kana ita ce muhimmiyar abokiya ta cinikayya ta kasashe da yankuna fiye da 150, da ta kiyaye zama kasa ta farko ta cinikin kaya na duniya, da kasa ta biyu da ke shigar da kayayyaki a kasuwannin duniya, kasar Sin ta zama muhimmiyar kasa da ta samar da kayayyaki da sayar da su a duniya.
Lin Jian ya kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga bunkasa tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, da tsaya tsayin daka kan manufar cin gajiyar bunkasar tattalin arziki tare da sauran kasashen duniya cikin adalci. Kasar Sin ta kiyaye bude kofa ga kasashen waje, da samar da yanayin yin kasuwanci mai kyau, da rage jerin sunayen kamfannonin da aka kayyade, don kara samar da kyakkyawar dama ga kamfanonin kasa da kasa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp