Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da fitar da biliyoyin kudi, domin fadada ayyukan raya gona 12 da ke fadin kasar nan, da nufin rage kalubalen yunwa, inganta samar da abinci da kuma habaka fannin aikin noma.
Daraktan Kudi na Hukumar Raya Koguna ta Hadejia Jama’are, Musa Iliyasu Kwankwaso ne ya sanar da haka, a ranar Asabar da ta ganbata a Jihar Kano.
- Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
- Jama’ar Duniya Sun Soki Matakin Amurka Na Matsawa Kasashe Ta Hanyar Kakaba HarajiÂ
Ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu; ya mayar da hankali wajen kara ciyar da yankin Arewa ta hanyar fannin aikin noma.
Kwankwaso ya yi nuni da cewa, aikin fadada raya kogunan zai kara taimakawa wajen samar da wadataccen abinci da rage yunwa tare kuma da habaka fannin aikin noma a fadin kasar.
Haka zalika, ya yaba wa Shugaban Kwamitin Kula da Kashe Kudi na Majalisar, Abubakar Kabir Abubakar Bichi, kan amincewa da fitar da kudin da za a gudanar da ayyukan.
Ya yi nuni da cewa, wannan amincewa ta Shugaban Kwamitin; daidai take da irin manufar Shugaban Kasa Tinubu, ta son kara bunkasa kasar nan kafin zuwan zabukan 2027.
Kwankwaso ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kan irin hangen nesansa, musamman wajen mayar da hankali kan samar da wadataccen abinci da kuma kokarin sake farfado da tattalin arzikin kasar.
Kazalika, ya yaba wa Shugaban Kwamtin kan gundunmawar da ya bayar wajen gainin an samar da wadannan ayyuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp