Matar Shugaban Majalisar Dattawa, Uwargida Ekaette Akpabio, ta shigar da ƙara biyu a gaban babbar Kotun birnin tarayya, Abuja, tana tuhumar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ɓata suna da take haƙƙinta na asali.
Matar Akpabio na neman diyyar Naira biliyan 250 da kuma Naira biliyan 1 don kuɗaɗen shari’a. Wannan na da nasaba da zargin cin zarafin da Natasha ta yi wa mijinta, Sanata Godswill Akpabio, yayin wata hira da Arise News a ranar 20 ga Fabrairu, 2025.
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe Naira Miliyan 998 A Cibiyoyin Ciyarwa Na Ramadan
- Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa
A ƙarar take haƙƙi (Suit No: CV/814/25), Matar Akpabio ta bayyana cewa maganganun Sanata Natasha sun saɓa wa hakkokinta da dokokin Nijeriya da kundin haƙƙin mutane na Afrika. Ta buƙaci kotu ta hana Natasha-Uduaghan ci gaba da yin irin waɗannan furuci tare da biyan diyya.
A wata ƙarin ƙara (Suit No: CV/816/25), Uwargidan Akpabio ta nemi kotu ta ayyana cewa zargin da Akpoti-Uduaghan ta yi na cin zarafin da mijinta ya yi mata ya ɓata mata suna da na iyalinta. Ta kuma buƙaci a tilasta Sanata Natasha ta janye kalamanta tare da buga bayar da haƙuri a jaridu biyu na ƙasa da kuma biyan Naira biliyan 1 a matsayin diyya.
Wannan shari’a na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce mai zafi tsakanin Sanata Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya jawo muhawara mai zafi a fadin ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp