Majiya daga Jami’ar Sojojin Nijeriya da ke Biu (NAUB) ta bayyana cewa, ana zargin Boko Haram/ISWAP da sace Shehun malamin Jami’ar, Farfesa Abubakar Eljuma tare da wasu fasinjoji, a ranar Lahadi.
Majiyar ta kara da cewa, lamarin ya faru ne a kan hanyar Damaturu zuwa Biu, kusa da kauyen Kamuya, wanda ya yi kaurin suna kan matsalolin garkuwa da mutane.
- NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN
- Natasha-Akpabio: Ƙungiyar Mata Ta Nijeriya Ta Gabatar Da Buƙatu Huɗu
Majiyar ta kara da cewa, Farfesa Eljuma, wanda shi ne shugaban bangaren koyon injiniyanci, kuma ya na daga cikin na gaba-gaba a takarar mukamin Shugabancin Jami’ar ( Vice-Chancellor ) da za a gudanar nan ba da dadewa ba.
Kauyen Kamuya ya na da nisan kimanin kilomita 10 daga kauyen Buratai, garin tsohon Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai (Rtd).
Lamarin dai ba shine karo na farko ba, domin an sha samun rahoton sace-sacen jama’a, fashewar bama-bamai da ake dasawa a kan hanyar, da kashe-kashe a yankin na tsawon shekaru 10 da suka gabata.
Ko a jiya Lahadi, 2 ga watan Maris, ana zargin Boko Haram da sace wasu matafiya da ba a tantance adadin su ba, a wasu motocin Golf guda 2 da bas daya (Borno Express) a kan hanyar Damaturu zuwa Biu.
Wani ma’aikacin Jami’ar NAUB wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da lamarin ga Wakilinmu a ranar Litinin, yana mai cewa, “shugabanin Jami’ar sun gudanar da wani taro mai muhimmanci game da sace Farfesan.” In ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp