Wani matashi mai shekara 20, Safiyanu Dalhatu, da ke unguwar Abujan Kwata a Bauchi, ana zarginsa da kashe mahaifiyarsa, Salama Abdullahi, mai shekara 40, ta hanyar dukanta da taɓarya.
Lamarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 3 na rana.
- Za A Kammala Aikin Titin Abuja-Kano Cikin Shekara 1 – Gwamnatin Tarayya
- Meranda Ta Yi Murabus, Obasa Ya Sake Zama Kakakin Majalisar Dokokin Legas
Bayan samun rahoton, ‘yan kwamitin tsaro na unguwa sun kai rahoto caji ofis ɗin ‘A’ Divisional.
DPO na caji ofis ɗin, CSP Abdullahi Muazu, ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa wurin da abin ya faru, inda aka garzaya da wacce aka jikkata zuwa asibitin ATBUTH da ke Bauchi.
Duk da ƙoƙarin likitoci, an tabbatar da mutuwarta.
Sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, ta bayyana cewa saɓani ne ya shiga tsakanin matashin da mahaifiyarsa, wanda ya haifar da tashin hankalin.
Majiyoyi daga unguwar sun ce matashin yana shaye-shaye, kuma mahaifiyarsa ta faɗa masa ya daina, wanda hakan ne ya fusata shi.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp