Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da kashe Naira miliyan 297 na shirin ciyar da buda baki na watan Ramadan na shekarar 2025, wanda aka tsara don samar da abinci ga mutane sama da 51,000 a kullum a duk tsawon watan Ramadan.
Ya ce shirin wanda ma’aikatar kula da harkokin addini da da’a ta kirkiro, ya fara ne da raba kayan abinci ga cibiyoyi 102 da aka kebe a fadin jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a madadin Kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Yusuf Umar, babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Yusuf Hassan Yusuf, ya bayyana kudirin gwamnati na ganin an aiwatar da shirin yadda ya kamata a fadin jihar.
Ya kuma bukaci kwamitin da ke da alhakin rabon kayayyakin da su hada kai da shugabannin al’umma da na addini a yankunansu domin ganin an raba kayan abincin yadda ya kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp