Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bitar rahoton aikin gwamnatin kasar, na tawagar lardin Jiangsu, a taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14.
Xi ya jaddada cewa, a matsayinsa na lardi mai karfin tattalin arziki, dole ne lardin Jiangsu ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ci gaban kasar Sin, musamman ma a fannin sa kaimi ga inganta kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da dunkulewar masana’antu, da sa kaimi ga inganta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa ga kasashen waje, da shigewa gaba wajen aiwatar da manyan tsare-tsare na ci gaban kasar, da kuma ba da misali a fannin samar da wadata ga jama’a baki daya. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp