Gwamnatin Jihar Sakkwato ta rage wa ma’aikata lokutan aiki a watan Ramadan domin sauƙaƙa musu gudanar da ibada cikin sauƙi.
A wata sanarwa da ofishin Shugaban ma’aikatan jihar, Sulaiman S. Fulani Ahmadu ya fitar, an bayyana cewa daga yanzu ma’aikata za su riƙa tashi daga aiki da misalin ƙarfe 2:30 na rana.
- Lin Jian Ya Yi Bayani Kan Takardar Bayani Game Da Shawo Kan Sinadarai Masu Alaka Da Sinadarin Fentanyl Ta Sin
- Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan sauyi ya shafi dukkanin ma’aikatan gwamnati, ciki har da na ƙananan hukumomi da malaman makarantun firamare, daga ranar Litinin zuwa Alhamis.
A ranar Juma’a kuwa, za su tashi da ƙarfe 12:00 na rana.
Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa Gwamna Ahmed Aliyu ne, ya amince da wannan mataki domin bai wa ma’aikata damar mayar da hankali wajen yin ibada a Ramadan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp