Hausawa na cewa, “idan kunne ya ji, jiki ya tsira.” Jama’a mu tambayi kanmu mana, wai me ke faruwa ne a kwanan nan tsakanin Amurka da ’yar goshin gabanta Ukraine? Amma kuma, za mu iya cewa, ba mamaki.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa, a cikin sa’o’i 24 zai kawo karshen yakin Ukraine da Rasha wanda kasarsa ta kasance gaba-gaba wajen bayar da tallafin kudi da makamai ga kasar Ukraine. A kan wannan yunkuri ne, tawagar Amurka ta gana da takwararta ta Rasha a birnin Riyadh na Saudi Arabiya, inda suka tattauna batutuwa masu dadi. Duniya ta yi jim tana ta sake-saken yadda za ta kare da ’yar lele (Ukraine) a yayin tattaunawar da aka dade ana tsumayi tsakaninta da uwargidanta (Amurka).
- Jami’an NDLEA Sun Kashe Budurwa A Kano, An Damƙe Su
- Sin Za Ta Kara Ingiza Samar Da Kudaden Gudanar Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu
Ganawar da Trump ya yi da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelenskyy, a ofishin Oval ta bai wa duniya mamaki, inda aka tashi ba tare da cimma wata matsaya ba, wanda hakan ke barazana ga makomar Ukraine musamman inda shugaban ya yi biris da maganar kwantiragin ma’adanai na kasarsa ga Amurka.
Wannan ziyarar ta bayyana wani hali na son kai na Amurka wanda ya fara dagula alakarta da kawayenta na yamma kunshe a matsayin “kariyar zaman lafiya” na gwamnatin Trump.
Don haka, shugabannin kasashen Turai suka gana a wani taro na gaggawa a birnin Paris a ranar Litinin domin mayar da martani kan sauyin manufofin Washington kan Kyiev, yayin da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, “Ana barazana ga tsaron Turai.”
Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta South Carolina, “sanadiyyar wannan ganawar da ta bar baya da kura, ka iya kawo karshen goyon bayan Washington ga Kyiv.”
Shin abin tambaya a nan, da gaske ne wannan yunkurin na Amurka don kawo karshen rikici ne a tsakanin Ukraine da Rasha ko kuwa don amfanin kanta ne? Me ya sanya gwamnatin Trump ta fara wani gangamin tonon silili mai zafi kan Zelenskyy?
Kwanakin baya sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya yi nuni da cewa, yunkurin Ukraine na shiga kungiyar NATO abu ne mara tabbas, tare da bai wa Kyiv shawarar daina fatan mallakar wani yankin kasa daga Rasha. Washington ta tattauna da Moscow a Saudi Arabia ba tare da Kyiev ba, wanda hakan ke nuna cewa za a iya yanke shawarar makomar Ukraine ba tare da saninta ba.
Bugu da kari, Trump ya kira Zelenskyy a matsayin “mai mulkin kama karya,” yana zargin Kyiv da fara tsokano rikici da Moscow. Sannan ya bukaci Zelenskyy ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ma’adinai da Amurka da sauri, in ba haka ba, zai iya rasa duka kasarsa ga Rasha. A yayin ganawarsu ta ranar Juma’a, Trump ya zargi Zelenskyy da yunkurin kawo yakin duniya na uku. Duk wannan barazanar don cimma muradan son zuciyar Amurka na matsawa Kyiev rattaba hannu kan yarjejeniyar ma’adanai.
Wannan a fili yake, Amurka tana son dawo da kudadenta na tallafin soji da ta bai wa Ukraine na tsawon shekaru ba don neman zaman lafiyar yankin ba.
Don haka, Trump ya ki la’akari da bukatar Zelenskyy na neman tabbatar masa da tsaro sai dai matsa masa kan amincewa da yarjejeniyar hakar ma’adanan Ukraine.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp