Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a aiwatar da matakan da suka wajaba na cimma nasarar tsare-tsare masu inganci, na bunkasa rundunar sojin kasar Sin na shekaru 5, wato tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojin kasar Sin, kuma sakataren kwamitin kolin JKS, ya yi wannan kira ne a Juma’ar nan, yayin da yake halartar taron rukuni na tawagar rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin PLA, da rundunar ‘yan sandan kasar, a wani bangare na taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp