Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana jimami kan rasuwar gogaggen ɗan jaridar nan, Malam Kabir Ɗangogo, wanda ƙwararren masanin aikin hulɗa da jama’a ne da aka ba lambobin yabo.
Haka kuma shi ne tsohon Sakatare-Janar na Ƙungiyar Aikin Hulɗa da Jama’a ta Afirka (African Public Relations Association, APRA).
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
- Kasar Sin Za Ta Kara Albarkatu Da Kudade Domin Tallafawa Samar Da Ayyukan Yi
Malam Kabir Ɗangogo dai ya rasu ne a Kaduna a ranar Juma’a da ta gabata, yana da shekaru 76. An yi jana’izar sa a Masallacin Sarkin Musulmi Bello bayan sallar Juma’a kafin a kai shi gidan sa na gaskiya.
An haife shi a ranar 21 ga Fabrairu, 1949, kuma ya yi karatu a Jami’ar Ohio da ke Athens a Amurka, a 1981, da Jami’ar Leicester ta ƙasar Birtaniya a 1987.
Ya yi aiki a kamfanin jaridun New Nigerian, da hukumar talbijin ta NTA, da Ofishin Yaɗa Labarai na Amurka (USIS). Haka kuma ya yi koyarwa a Kaduna Polytechnic, ya yi aiki a Bankin Arewa da kuma Bankin Union inda a nan ya yi ritaya a ranar 26 ga Yuni, 2005.
A cikin saƙon ta’aziyyar sa a ranar Asabar, Minista Idris ya bayyana rasuwar Malam Kabir Ɗangogo a matsayin babban rashi ga Nijeriya da fannin sadarwa a nahiyar Afirka.
Ya ce: “Mutuwa ta ƙwace mana ƙwararren ma’aikaci wanda ke da cikakkiyar sadaukarwa ga aiki, da ƙwarewa a aikin jarida, da kuma gagarumar gudunmawar da ya bayar a fannin hulɗa da jama’a.
“Ta hanyar aikin sa, ya ɗaga martabar hulɗa da jama’a a Afirka, inda ya jagoranci ci gaba da tabbatar da ɗa’a, horar da ƙwararru, da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe.”
Ministan ya yaba wa Ɗangogo a matsayin jagora, mai hangen nesa, kuma uba ga masu aikin hulɗa da jama’a (wato public relations), wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta fannin a Nijeriya da Afrika baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa a lokacin da Ɗangogo ke riƙe da muƙamin Sakatare-Janar na APRA, ya jajirce wajen ƙarfafa tattaunawa, da fito da sababbin abubuwa, da kuma ci gaba da tabbatar da ɗa’a a ɓangaren sadarwa da kula da suna.
Ya ce: “A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalan sa, abokan aikin sa, da ɗaukacin ‘yan jarida da masu hulɗa da jama’a.
“Ina roƙon Allah ya gafarta masa, ya jiƙan sa, ya kuma ba iyalan sa haƙurin jure wannan babban rashi.”
Ministan ya kammala da cewa gagarumar gudunmawar da Ɗangogo ya bayar za ta ci gaba da zaburar da sababbin ‘yan jarida da masu aikin hulɗa da jama’a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp