Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta soki kalaman sakataren baitul-malin Amurka da ya bayyana dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu a matsayin zamba.
An shafe gomman shekaru ana huldar cinikayya tsakanin bangarorin biyu, a gani na, idan har akwai zamba a ciki, ba na jin huldar za ta kawo matakin da take kai a yanzu. Abun da Amurka ta kasa ganewa shi ne, ita kanta da sauran duniya sun fi bukatar Sin. Idan Amurka ta ci gaba da ta da yakin cinikayya, sai ta fi kowa dandana radadin matakanta, la’akari da yadda kayayyakin kasar Sin suka bunkasa sayayya a kasar. Kana masana sun yi hasashen munanan matakan, za su haifar da raguwar GDPnta da hauhawar farashin kayayyaki da rashin ayyukan yi a kasar da sauransu.
- Bayan Shekaru 115 Manchester United Za Ta Gina Sabon Filin Wasa
- Zafin Rana Zai Tsananta A Wasu Jihohin Nijeriya – NiMet
Abun da ya kamata Amurka da kawayenta su gane shi ne, kasar Sin ta fi mayar da hankali kan habaka bukatun cikin gida domin karfafa tattalin arzikinta maimakon dogaro da kasashen waje. Matsin da Amurka ta dade tana yi wa kasar Sin, ya kara tabbatar da cewa, tattalin arzikin Sin ba ya dogaro da kasashen waje, bisa la’akari da yadda matsin bai sa tattalin arzikin ya durkushe ba, maimakon haka, ya zama wani karin zaburarwa ga kasar Sin ta nacewa ga habaka bukatun cikin gida da kirkire-kirkire, domin biyan bukatunta da na sauran kasashe duniya.
Yayin gabatar da rahoton aikin gwamnati ga majalisar dokokin kasa a makon jiya, firaministan Sin Li Qiang ya ce kasar na da burin habaka tattalin arzikinta da kaso 5 cikin dari a bana, lamarin da ya ja hankalin duniya matuka. Hakika wannan buri da ta sanya gaba, ya kara bayyanawa duniya kwarin tubalin tattalin arzikinta da kuma irin ci gaba da za ta samu. Har kullum na kan ce, ci gaban kasar Sin, ci gaba ne ga duniya baki daya. A matsayinta na babbar abokiyar cinikayya ta kasa da kasa, kuma cibiyar kirkire-kirkire a duniya, kana mai bayar da gudummawar kaso 1 bisa 3 na ci gaban tattalin arzikin duniya, karuwar tattalin arziki da ci gaban Sin babbar dama ce kuma abun murna ga kasashe musamman masu tasowa. (Faeza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp