Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta gargaɗi al’umma cewa za a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin har tsawon kwanaki huɗu.
Jihohin da za su fi fuskantar wannan zafi sun haɗa da Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa, da Benuwe.
- Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari
- Gina Mutane Don Bunkasa Hazakarsu Na Daga Cikin Ajendar Sin Na 2025
Haka nan kuma Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi, Kuros Riba, da Birnin Tarayya, Abuja su ma za su fuskanci zafin rana mai tsanani.
Sauran jihohin sun haɗa da Taraba, Adamawa, Filtao, Kaduna, Zamfara, da Sakkwato.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Abuja, NiMet ta shawarci mutane da su guji fita lokacin tsananin zafi, musamman daga ƙarfe 12 na rana zuwa 3 na yamma.
Haka kuma, an bukaci su riƙa shan isasshen ruwa, amfani da fanka ko na’urar sanyaya ɗaki, da kuma zama a wurare masu inuwa don kaucewa illar zafi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp