Shugaban kungiyar Zumunta da Taimakon Jama’a, ‘’Community Debelopment Association’’ da ke garin Tafa ta karamar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, Alhaji Maikudi Dogo, ya yi kira ga al’ummar garin, da kada su sare wajen cigaba da zumunci da zamantakewar da aka san su dashi shekara da shekaru a tsakaninsu.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake hira da manema labarai yayin gudanar da babban bikinsu na Ajo da suka saba shiryawa akai-akai a harabar ofishin kungiyar da ke garin na Tafa a karshen mako, inda ya yi nuni da cewa, sada zumunci da taimakon juna da al’umma baki daya, sune makasudin kafa kungiyar.
- Martanin El-Rufa’i: Ko Gawata Ba Za Ta Kusanci PDP Ba
- “Korar Fulani A Edo: Ina Ake So Wadanda Aka Haifa A Jihar Shekara 50 Su Koma?”
Ya kuma ce, yau shekara sama da 20 kenan da suka kafa kungiyar, a lokacin da membobi 60 kacal, amma yanzu, membobin kungiyar sun haura mutum 200 maza da mata da matasa wadanda suka fito daga jihohi daban-daban na fadin kasar nan, yana mai cewa, ” Alhamdu Lillahi, kungiyar cikin shekarun nan, ta tallafa wa membobin ta da dama ta hanyoyi daban-daban, kamar taimako wajen daurin aure, marasa lafiya, jarin yin kasuwanci da sauran su”.
Alhaji Maikudi sai ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta waiwaye su, ta taimakawa kungiyar da irin tallafin da take baiwa kungiyoyi a jihar, saboda gagarumin taimakon da take yi wa jama’a musamman marasa galihu, da kuma hobbasar da take yi wajen hada kai da jamai’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a Tafa.
A tasu gudunmawar, mataimakin kungiyar, Alhaji Haladu Musa Usman da kakakin kungiyar (PRO) Alhaji Salisu Hassan, duk kira suka yi ga Gwamnati da ta tallafa wa kungiyar saboda taimakon jama’a da take tayi shekara da shekaru.
Ita ma Shugabar mata, Hajiya Ladidi Kabuga, kira ta yi ga membobin kungiyar, maza da mata, da suci gaba da bin dokokin kungiyar, su kuma zama masu ladabi da biyayya, har ila yau, su kasance masu Kyakkyawar zamantakewa a tsakanin su.
An dai tashi bikin lami lafiya. Cikin manyan bakin da suka halarci bikin akwai Alhaji Danladi Obajana, Alhaji Baffa na ‘yan Canji, Alhaji Musa mai Shadda, Alhaji Abubakar mai DubuDubu, Alhaji Wawan Sarki, Hakimi Uban Badodo daga Bauchi, da Alhaji Dilan fata daga Gombe. Wasu kuma sune, Hajiya Maimuna kawo daga Kano; Hajiya Maryam Oka.
Jamila Gombe; Hajiya Jummai daga Mokwa, da Hajiya Fati Cestelo daga Mararrabar Jos. Sauran sun hada da Usaina daga Mararrabar Jos, Hajiya Bilki daga Kano, da kuma Hajiya Aisha daga Bauchi