Wani gungun mayakan Boko Haram sun yi yunkurin afkawa ayarin motocin Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a kan hanyar Buni- Gari zuwa Buni Yadi, yayin da jami’an tsaron suka kashe wasu yan ta’addan da ba a tabbatar da adadinsu ba, tare da ceto wasu fasinjoji 7 da aka sace.
Wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa, ayarin wanda ya hada da sojojin Operation Hadin Kai, rundunar ‘yansanda tare da manyan jami’an gwamnati, suna kan hanyar su ne ta dawowa daga karamar hukumar Biu, inda suka ci karo da ‘yan ta’addan a sa’ilin da suke kokarin yin garkuwa da wasu matafiya a wata mota, kirar Golf.
- Yawan Bishiyoyin Da Aka Dasa A Kasan Kasar Sin Ya Kai Kashi 25%
- Muddin Nahiyar Afirka Ta Farka Ba Za A Iya Raina Ta Ba
Gwamna Zulum, ba ya cikin ayarin motocin, inda ya dawo birnin na Maiduguri ta jirgin sama, a lokacin harin.
Ganin halin da fasinjojin ke ciki, sojojin suka yi kukan kura kan yan ta’addan, inda hakan ya tilasta suka saki fasinjojin da suke yunkurin garkuwa dasu tare da arcewa zuwa cikin daji.
Hakan ya sanya Sojojin kutsa kai cikin dajin domin farautar yan ta’addan, al’amarin da ya basu nasarar halaka wasu yan ta’adda da kwato makamai da babura.
Bugu da kari kuma, babu ko mutum daya a cikin ayarin da ya samu rauni ko kwalzani, amma daga bisani sun kubutar da fasinjojin guda 7.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp