الشُّكْرُبِاللِّسَانِ: هُوَ الثَّنَاءُ عَلَى الْمُنْعِمِ، وَالتَّحَدُّثُ بِالنِّعَمِ. قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: “التَّحَدُّثُ بِالنِّعَمِ شُكْرٌ”. وَالشُّكْرُ بِالْجَوَارِحِ: هُوَ الْعَمَلُ بِطَاعَةِ اللَّهِ، وَتَرْكُ مَعَاصِيهِ. وَالشُّكْرُ بِالْقَلْبِ: هُوَ مَعْرِفَةُ مِقْدَارِ النِّعْمَةِ، وَالْعِلْمُ بِأَنَّهَا مِنَ اللَّهِ وَحْدَهُ، وَالْعِلْمُ بِأَنَّهَا تَفَضُّلٌ، لَا بِاسْتِحْقَاقِ الْعَبْدِ.
Fassara:
“ Godiya ga Allah da harshe: Na nufin yabon Mai ni’ima da kuma bayyana ni’imomin da ya bayar. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Bayyana ni’imomi yana daga cikin godiya.” Godiya da gaɓɓai kuma: Na nufin yin aiki da biyayya ga Allah da barin saɓa Masa. Godiya da zuciya kuma: Yana nufin sanin girman ni’ima da fahimtar cewa daga Allah take Shi kaɗai, kuma da sanin cewa yana bayar da ita ne a matsayin kyauta, ba don bawa ya cancanta ba.”
Fashin Baƙi:
Wannan magana ta Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, tana bayani ne a kan ma’anar godiya ga Allah (wato ash-Shukru) da sassanta uku da take da su:
1. Godiya da harshe:
Wannan yana nufin yabon Allah da faɗar ni’imominsa da kuma ambatonsa a cikin kalmomi. Wannan yana da muhimmanci saboda yana nuni da cewa mutum ya gane cewa Allah ne mai bayar da ni’ima. Hadisin da aka kawo yana nuna cewa mutum idan ya bayyana ni’imomin Allah, to yana cikin masu godiya. Wannan na iya kasancewa ta hanyar zikirai, du’a’i, da yabonsa da albarkar da yake bayarwa, da cewa Allah Ya yi min ni’ima iri kaza da kaza.
2. Godiya da gaɓɓai:
Wannan yana nufin amfani da dukkan gabban jiki wajen yin biyayya ga Allah da nisantar saɓon Sa. Misali, idan mutum yana da lafiyar jiki, to ya yi amfani da lafiyar wajen aikata kyawawan ayyuka kamar sallah, azumi, sadaƙa, da taimakon jama’a. Idan kuma mutum yana da arziki, ya yi amfani da shi wajen tallafa wa marasa hali da hidimtawa addini. Wannan yana tabbatar da cewa godiya ga Allah ba kawai yana cikin harshe ba, har ma yana cikin aiki.
3. Godiya da zuciya:
Wannan yana da alaƙa da imani da ilimi. Yana nufin mutum ya gane cewa duk wata ni’ima daga Allah take, ba wai saboda ya cancanta a ba shi ba saboda wani abu da ya yi wa Allah, a a sai dai domin Allah yana da rahama da falala da jin ƙai. Wannan yana hana girman kai da alfahari, domin mutum zai fahimci cewa Allah Yana bayar da ni’ima a matsayin kyauta, ba lallai ne saboda ibadarsa ba. Wannan yana ƙarfafa tawali’u da jin haƙuri idan mutum bai samu abin da yake so ba.
A taƙaice, maganar Ibnu Juzai tana koyar da cewa godiya ba kawai fadar “Alhamdulillahi” ba ce kawai, a a, tana da sassa guda uku: da suka haɗa da harshe, da aiki, da kuma zuciya. Idan mutum yana godiya ta waɗannan hanyoyi, to zai zama cikakken mai godiya ga Allah. Wannan yana ƙarfafa imani, yana ƙara ni’ima, kuma yana kusantar da bawa ga Ubangijinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp