Shugaban kasa Bola Tinubu, ya shaida cewar ya cire tallafin mai ne domin kare makoman al’umman da za su zo nan gaba wato matasa Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya shaida hakan ne a wajen kaddamar da kwamitin shirya babban taron matasa na kasa domin budada hanyoyin janyo matasa cikin sha’anin mulki da nema musu ayyukan yi wato ‘National Youth Congress Planning’ da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- ’Yan Adawa Na Kitsa Makarkashiyar Tsige Ni – Akpabio
- Jami’in Sin: Ba Za A Lamunci Ayyukan ‘Yan Aware Na “Ballewar Taiwan” Ta Ko Wace Hanya Ba
Tinubun ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar wa matasa da ayyukan yi, ya shelanta cewa manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa ana shirya su ne da zimmar taimaka wa rayuwar gobe.
“Lokacin da aka cire tallafin mai, kana kare rayukan gaba ne na yaran da ba a haifa ba, matasa.
“Ina zuba jari don kayayyakin more rayuwa? Lokacin da kuka saurari yawancin kwararru suna magana game da Japa, barin Nijeriya, saboda idan kun samu wadata a gida kuma kun karfafa mutane, ba za su damu da barin ba, za su zauna a gida. Wannan shi ne gidan ku, don habakawa, ginawa da wadata.
“Gwamnati gaba daya ta dogara ne kan yadda za ta kyautata rayuwar jama’a, mun dauki lamarin matasa da muhimmanci sosai.”
Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatinsa a kowani lokaci a shirye take wajen yin ayyukan tukuru domin kyautata rayuwar matasa da saukaka matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.
Kan kwamitin da ya kaddamar, Tinubu ya kalubalancesu da su yi aiki tukuru domin ganin rayuwar matasa ya samu tagomashi a kowani lokaci.
Shi kuma a jawabinsa, ministan bunkasa harkokin matasa, Ayodele Olawande, ya ce, kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin an samu inganta shigo da matasa cikin sha’anin mulki.
Olawande ya lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce mai saurare da ke shirye ta mai da hankali tare da hada ra’ayoyi da gudummawar matasa a cikin shugabanci.
Ya ce an zabo mambobin ne a hankali a matsayin wakilai daga ma’aikatar kudi ta tarayya, sauran ma’aikatun tarayya masu alaka, kungiyoyin farar hula, kungiyoyi masu zaman kansu na bankin duniya da dai sauransu.
Ya ce za su jajirce da tsara taron da zai yi tasiri a rayuwar matasan Nijeriya.
Wani jigo a kwamitin tsare-tsare na matasa kuma Babban Darakta na Yiaga Africa, Samson Itodo, ya yaba da jajircewar Shugaba Tinubu na karrama matasan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp