Babu shakka, a wancan lokaci na mulkin mallaka, ba a bar wa jama’ar kasa cikakken ikon zabar “yan majalisu ba, face an yi kokarin shigo da wasu ka’idojin na karara a zahiri, sun nuna wariyar jinsi ne, kuma zaben, an cire shi ne ma daga hannun talakan kasa kacokan, sai masu hannu da shuni ne ke da cikakken ikon zabar kunshin “yan majalisun lardunan kasar da suke da muradi.
Cikin wadancan ka’idoji na zabe, da farko an fadi cewa, wanda ke da ikon yin zabe, dole ne ya kasance mutum namiji, kuma baligi, wanda yake mazauni ne a wannan yanki ko muhallin zabe na akalla tsawon Shekara guda. Dadin dadawa, wajibi ne shi wannan mai zabe, ya zamana ya mallaki adadin fam dari (€100) na kudin Ingila (miliyoyin kudade ne da za a kwatanta kimarsu a yau). Ke nan, shi ma baturen da farko ya yarda da fifiko tsakanin namiji da mace! Don me ya sanya bai bai wa mata cikakken “yancin yin zabe a farkon lamari cikin wannan kasa, tamkar irin yadda ya bai wa maza?. Ba ya ga banbanta jinsin maza da na mata, don me kuma ya sanya aka sake banbanta hakkin yin zabe a tsakanin mawadata da talakawa?. Ko mene ne dalilin nasu, ba a kan wannan ne ake yin wannan rubutu ba, saboda haka, za mu fuskanci mafuskantar rubutun ne ta tun-azal.
Ba ya ga irin wadancan banbance-banbance da Turawan Birtaniya suka fara tsirarwa a tsakanin masu zabe, sai suka lallaba, tare da afkar da wani irin banbanci hatta a tsakanin “yan majalisun kansu. Babu shakka, tsarin mulkin Kilifod, ya nuna yunkurinsa na kawo rarrabar kawunan jama’ar lardunan kudanci da na arewacin wannan kasa, a kan hanyarsa ta shimfida mulki yadda ya so cikin dabaru. Saboda makirci irin na “yan mulkin mallakar, sai aka wayi gari, sun bai wa “yan majalisun lardin kudancin kasar, damar yin dokoki ga mutanensu. A daya hannun kuwa, maimakon bai wa “yan majalisun lardin arewacin kasa irin waccan damar tamkar yadda aka bai wa takwarorinsu na kudanci, sai aka karbe ikon yin dokokin daga hannunsu, aka danka a hannun gwamna Bature. Aka wayigari gwamna Bature ne zai rika yi wa jama’ar arewacin kasar doka, ta hanyar shelantawa. Duk abinda gwamna ya shelanta a arewacin kasar, da sunan wata doka, shike nan, shi ne za a rika a matsayin dokoki ga al’umar yankin lardin arewa!!!. Sai kuma aka yi wani kwan-gaba kwan-baya cewa, duk da an kwace ikon yin dokokin daga hannun “yan majalisun na arewa zuwa hannun gwamna, sai kuma aka ce “yan majalisun na arewa na da ikon yin dokokin da suka shafi sabgar batar da kudade na gwamnati.
Duk da an bai wa “yan majalisun arewar damar yin doka game da sabgar bad da kudin, mu sani cewa, idan majalisar za ta zauna, za ta zauna ne tare da gwamnan lardin arewa Bature. Bayan shi, da akwai ma wasu mutane Turawa da za a zauna da su, wadanda ke cikin kunshin hukumar harkokin kasuwanci da masana’antun ma’adanai ta Kano, a matsayinsu na mambobin majalisar, kamar yadda aka bayyana a baya.
Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike musu kugu ne, ta yadda za a ga ba su da wani tasiri ko katabus, wajen zuwa da kyawawan manufofi, don ciyar da jama’arsu gaba. Yanzu kuwa, za a iya yi wa wadannan “yan majalisun uzuri?.
Shin, suna da cikakken ikon gudanar da aiyukan nasu ko babu?. Babu shakka, duk wani irin iko da ake da bukata da tsarin mulki zai ba da, ya jima da bai wa “yan majalisun namu wannan iko ko dama a yau. To a ina ne yanzu gizo ke sakar? Cikin batutuwan da za a bijirar gaba, a nan ne kowa ke da ikon yin tsifa game da gurbacewar al’amuran majalisa a Nijeriyar yau.
“…The composition and functioning of the legislatibe council, howeber, pointed to the fact that, it was nothing more than a mere rubber-stamping institution…”.
(Fagge & Alabi, 2007: 5b).
Wadancan kalamai na sama cikin harshen Turanci, na yin nuni ne da cewa, “yan majalisun Nijeriya a wancan lokaci da Turawan Birtaniya ke mulkarmu, ba su kasance komai ba, face “yan-abi-yarima ne cikin harkokin zaman majalisar. Duk abinda aka yanke a majalisar, kawai sai dai su sanya-hannu ne akai. Ba su da ikon tabbatar da wani kudiri, koko yin watsi da shi. Tun da, hatta mafi yawan adadin mutanen da ke cikin zauren na majalisar, za a samu cewa, gwamna ne ya zabe su da hannunsa, kamar yadda a rubutun baya aka faiyace irin adadinsu dalla-dalla.
Batun rashin iko, ko karancinsa, shi ne babban abinda ya mamaye harkokin “yan majalisun na kasa gabanin Nijeriya ta kai ga samun “yancin-kai. Sai dai, a kan samu wasu “yan canje-canje ne daga lokaci zuwa lokaci, sakamakon mabanbantan kundin tsarin mulkin da Turawan suka gabatar mana da su gabanin kai wa ga samun yancin-kai. Tulin labaran “yan majalisun na da auki ainun, kawai za mu yi kokarin matsawa gaba ne cikin hanzari, don kai wa ga yadda lamuran majalisar ke wakana a yau, wanda shi ne babban abinda muke son yin doguwar tattaunawa akai sannu a hankali.
“Yan Majalisunmu A Shekarar 1900
Ya tabbata, bayan samun “yancin-kai a wannan Kasa (cikin Shekarar 19b0), “yan majalisun namu, sun kai ga fara samun “yancin gudanar da aiyukansu, sama da irin yadda suka kasance a baya. Tsarin mulki irin na shugaban kasa daban, da shugaban gwamnati (tsarin mulkin firaminista) daban, aka fara dabbakawa a wannan kasa bayan samun mulkin kai. A karkashin tsarin mulkin, za a ga irin aikace-aikacen da wadannan ‘yan majalisun namu na lokacin suka gudanar, kafin juyin mulkin Soja na farko da aka fara yi a kasar, cikin Shekarar 19bb, Shekaru shida (b) kacal, bayan samun yancin-kai. Ke nan, irin ayyukan da suka gudanar cikin majalisar, zai zamto ne a tsakanin Shekarar 1900 da Shekarar 1900.
Ga wasu daga irin ayyukan da bangaren “yan majalisun suka gudanar kamar haka;
i- Kafa Gwamnati: “yan majalisun ne suka taka rawa wajen zabar firaminista Abubakar Tafawa Balewa a matsayin shugaban gwamnati, tare da yunkurin fasalta tsarin gwamnatin dimukradiyya.
ii- Ci gaban bangaren dokoki: “yan majalisun, sun samar da dokoki kyawawa, musamman wadanda suka shafi ci gaban tattalin arzikin kasa, ilimi tare da samun cikakken ikon gudanarwa a cikin lardunan kasar da ake da su.
iii- Kyautata Wakilci A Gwamnatin Hadaka Da Na Larduna: tsarin, ya ba da dama ga jagororin gwamnati (firimiyoyi) na lardunan arewa da yamma da na gabashin kasar, na su shigo cikin lamuran gudanar gwamnati dumu-dumu, don a dama da Canji
iv- Canjin Mirginawar Tsarin Mulki Na Kasa: “yan majalisun, sun taka rawa muhimmiya, wajen dawowar tsarin mulkin dake nuna lamuran Kasar, na gudana karkashin ikon Sarauniyar Birtaniya ne, zuwa ga wata jamhuriya mai zaman kanta cikin Shekarar 19b3, wadda ikonta ya sabbawa Dr Nnamdi Azikiwe zama shugaban kasar Nijeriya na farko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp