Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da ya sake sabunta albashin ma’aikata don kara albashin zuwa kashi 50 cikin 100, idan aka yi la’akari da yadda rayuwa take tafiya a kasar nan.
Ta bayar da wannan shawarar ce a cikin wasikar da shugaban NLC na kasa Ayuba Wabba ya rattaba wa hannu ya kuma tura wa Buhari.
Wasikar mai dauke da kwanan wata 8 ga watan Agustan 2022, kungiyar ta bayar da wannan shawarar ce biyo bayan shawarar da kungiyar gwamnonin kasar ta bai wa Buhari na yiwa ma’aikatan da suka haura shekaru 50 ritiya daga aiki.
Kungiyar wacce ta soki gwamnonin kan wannan sahawara ta su, ta sanar da cewa, maimakon a yiwa ma’aikatan ritaya, kamata ya yi ace gwamnatin ta kara musu albashi.
NLC ta kuma jinjina wa shugaba Buhari kan karin albashi mafi karanci na ma’aikatan gwamtin tarayya.