Bayan da hukumar gwamnatin kasar Sin ta fitar da alkaluman tattalin arziki na watanni biyu da suka gabata a jiya Litinin, kafofoin watsa labarai na kasashen waje, kamar Jaridar Wall Street, sun jinjinawa gagarumin ci gaba mai ban mamaki da Sin ta samu a fannonin kashe kudi, da raya masana’antu da dai sauransu.
To ko me ya sa suka bayyana hakan? Akwai dalilai guda biyu. Na farko shi ne Sin ta bunkasa tattalin arziki cikin kwanciyar hankali. Inda a watanni biyu da suka gabata, saurin karuwar yawancin manyan alamomin tattalin arziki na Sin ya samu ci gaba, idan aka kwantanta da shekarar bara baki daya.
- Sin Na Adawa Da Haramta Amfani Da DeepSeek Da Gwamnatin Amurka Ta Yi
- Trump Zai Tattauna Da Putin Kan Kawo Ƙarshen Yaƙin Ukraine
Alal misali, yawan karuwar masana’antu masu babban ma’auni na kasar ya kai kashi 5.9 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara, inda saurin karuwarsa ya kai kashi 0.1 bisa dari kan na shekarar bara baki daya, kuma saurin karuwar zuba jari kan kadarori ya karu da kashi 0.9 bisa dari, idan aka kwantanta da na shekarar bara baki daya. Bisa wadannan alamomi, ana iya ganin cewa tattalin arzikin Sin ya kiyaye yanayin farfadowa, tun daga kwata ta hudu ta shekarar bara, kuma ya kasance cikin yanayi mai nagarta.
Na biyu shi ne, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da karuwa a fannin fasahohin zamani. A cikin watanni biyu da suka gabata, saurin karuwar darajar masana’antun kere-keren fasahohin zamani na kasar, ya karu da kashi 0.2 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara, inda saurin karuwar zuba jari na masana’antun fasahohin zamani ya fi samun saurin karuwar zuba jari baki daya, wanda hakan ya nuna cewa, sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko na ci gaba da bunkasuwa cikin kwanciyar hankali.
Bisa irin wadannan nasarori da Sin ta cimma, a cikin wani dan lokaci, kafofin watsa labarai na waje sun yaba da karsashin tattalin arzikin kasar Sin sosai.
Jaridar Financial Times ta Burtaniya ta bayyana cewa, masu zuba jari na kasashen waje suna kara “gano kasar Sin”, kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin za ta iya samar da “kirkire-kirkire da damammaki” masu yawa a wasu fannoni. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp