Kasar Sin tana maraba da duk kokarin da ake na tabbatar da tsagaita bude wuta a rikicin Rasha da Ukraine, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labarai na yau Laraba, a tsokacinta game da tatattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Donald Trump. Tana mai cewa, kasar Sin ta kasance tana ba da shawarar warware rikicin ta hanyar tattaunawa da shawarwari.
Kuma “Muna farin cikin ganin duk wani kokarin da zai kai ga tsagaita bude wuta, muna ganin wannan a matsayin wani matakin da ya dace don samun zaman lafiya,” a cewar Mao.
A tattaunawarsu ta wayar tarho a ranar Talata, Putin da Trump sun amince cewa, za a maido da zaman lafiya a Ukraine “da fara tsagaita wuta a bangaren makamashi da kayayyakin more rayuwa.”
Da aka tambaye ta game da sabbin takunkumin biza da Amurka ta kakaba wa Cuban, Mao Ning ta ce, Sin na adawa da matakin tilastawa ta hanyar diflomasiyya, ta kuma bukaci Amurka da ta gaggauta dakatar sanyawa kasar Cuba takunkumi, tare da cire Cuba daga cikin jerin kasashen da ta kakaba wa takunkumin na cewar suna daukar nauyin ta’addanci. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp