Mahaddatan Alkur’ani da dama ne suka hadu a masallacin Juma’a na Sheikh Isayaka Rabiu da ke Goron Dutse domin yi wa kasa addu’a ta musamman saboda matsalar tsaro da ake fuskanta.
Malaman sun gudanar da saukar Alkur’ani mai tsarki 2,444 tare da addu’ar neman zaman lafiya a Kano da ma kasa baki daya.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Mana Tayin Miliyan 10 Mu Saki ‘Yan Uwansu Amma Mun Ki Karba – NSCDC
- Gajartar Amarya Tasa Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Ana Tsaka Da Gudanar Da Biki
An dai gudanar da taron addu’ar ne, karkashin jagorancin Khalifa Nafi’u Ishaq Rabiu.
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala karatun, gwani Yusuf Ishaq Rabi’u, ya ce babu wata matsala da za ta tunkari jama’a da alkur’ani ba zai magance ta ba.
Don haka, ya bukaci masu hannu da shuni da ‘yan siyasa su dinga shirya irin wadannan taruka na addu’a domin nema wa kasa zaman lafiya.
Ya kuma gode wa malaman da suka gabatar da saukar tare da bai wa al’umma karfin gwiwar cewa Allah zai karbi bukatunsu.