Yau ne, aka bude bikin baje kolin kasa da kasa kan hanyar siliki karo na shida wato taron tattaunawa kan yin hadin gwiwa da zuba jari da yin cinikayya tsakanin gabashi da yammacin kasar Sin a birnin Xi’an.
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Yang Jiechi ya halarci bikin bude taron, tare da gabatar da jawabi.
A jawabin nasa, Yang Jiechi ya bayyana cewa, kusan shekaru 9 ke nan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kuma ya zuwa yanzu, ta samu ci gaba mai inganci gami da manyan nasarori.
Haka kuma shawarar ta samu karbuwa tsakanin al’ummomin duniya, ta zama dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, wadda ta nuna karin kuzri da jan hankali.
Kasar Sin tana kira ga dukkan bangarori da su taimakawa juna, da shawo kan matsaloli tare, da kiyaye rayuwar bil Adama tare, da kiyaye lafiyar jama’a, da karfafa ginshikin cudanya da hadin gwiwa, da fadada sabbin fannonin hadin gwiwa tare, da gina muhimman ayyuka na rayuwa cikin hadin gwiwa, da zurfafa shawarar.
Idan aka hada kai tare da yin hadin gwiwa, hakika, tattalin arzikin duniya zai farfado ya kuma habaka nan da nan, har ma a yi kokarin gina shawarar “ziri daya da hanya daya” a matsayin “ziri na ci gaba” wanda zai amfanar da duniya baki daya da samar da “hanyar farin ciki” wadda za ta amfani jama’ar dukkan kasashe. (Ibrahim)