Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
Jakadan Sin dake kasar Rasha, Zhang Hanhui da wakilan bangaren siyasa da ba da ilmi da yada labarai na kasar Rasha sun halarci taron don tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da musanyar al’adu da kuma hadin kan kafofin yada labarai da sauransu. Wakilai na Rasha sun hada da Andrey Denisov, mataimakin shugaba na farko na kwamiti mai kula da harkokin ketare na tarayyar kasar Rasha, da kuma Alexander Yakovenko, mataimakin babban manajan rukunin yada labarai na“Rossiya Segodnya”,kana da Andrey Margolin, mataimakin shugaban kwalejin nazarin tattalin arziki da harkokin al’umma dake karkashin shugaban Rasha wato (RANEPA), da Yuri Mazei, mataimakin shugaban jami’ar Lomonosov Moscow, kana da Mikhail Chkanikov, babban editan jaridar “Arguments and Facts”. (Amina Xu)














