Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya), ya naɗa Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar.
Wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Jiha, Dakta George Nwaeke.
- An Ceto ‘Yan Nijeriya Sama Da 950 Daga Gidajen Yari A Libya – Gwamnati
- Ministan Lafiya Ya Yi Alƙawarin Inganta Tallafi Ga Likitoci A Hajjin 2025
Ba a bayyana dalilin murabus ɗinsa ba, amma shugaba Ibas ya gode masa bisa gudunmuwarsa ga jiharsa tare da masa fatan alheri.
A halin yanzu, Iyingi Brown, Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikatan jihar, zai riƙe muƙamin a matsayin na riƙon ƙwarya har sai an naɗa sabon shugaba.
A cikin wata sanarwa, Ibas ya bayyana cewa naɗin Farfesa Worika zai fara aiki nan take.
A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa.
Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya.
Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro.
Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp