Darakta a ofishin lura da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da mataimakin shugaban kwamitin kasa na Amurka mai lura da alakar Sin da Amurka Evan Greenberg.
Yayin da suke zantawa a yau Laraba, Wang ya jinjinawa Greenberg, bisa tsawon lokaci da ya shafe yana ingiza tattaunawa, da hadin gwiwa tsakanin bangaren Sin da na Amurka, yana mai fatan kwamitin kasa na Amurka mai lura da alakar Sin da Amurka, da sauran kwararru daga dukkanin fannonin rayuwa na Amurka, za su bayar da sabbin gudummawa don wanzar da daidaito, da tabbatar da kyakkyawar alakar Sin da Amurka yadda ya kamata.
A nasa bangare kuwa, mista Greenberg ya ce alakar Sin da Amurka ita ce mafi muhimmanci tsakanin alakokin wasu kasashe 2 na duniya. Don haka ya dace sassan biyu su yi amfani da kwarewa da basirarsu, wajen inganta fahimtar juna, da fadada hadin gwiwa da zaman jituwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp