A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana karɓar baƙuncin shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama a fadar shugaban kasa dake Abuja, yayin da shugabannin biyu ke ganawa domin ƙarfafa hulɗar diflomasiyya.
Shugaba Mahama ya isa fadar shugaban kasa ne da misalin karfe 2:30 na ranar Alhamis, a ziyarar aiki ta farko a Nijeriya tun bayan rantsar da shi a ranar 7 ga watan Janairu, 2025.
- Wakilin Sin: Dole Ne A Mutunta Hakki Mai Tushe Na Palasdinawa
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC
Ana sa ran taron zai mayar da hankali ne kan zurfafa alakar da ke tsakanin kasashen Afirka ta Yamma, inda za a tattauna batun kasuwanci, tsaro da hadin gwiwar tattalin arziki.
Ana kuma sa ran tattaunawar za ta kunshi ci gaban yankin a cikin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, inda shugabannin biyu suka yi alkawarin ciyar da zaman lafiya da gudanar da mulkin dimokradiyya.
A baya, Mahama ya ziyarci shugaba Tinubu jim kadan bayan lashe zaben shugaban kasa a watan Disamba na 2024.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp