Hukumar ‘yansanda a Jihar Adamawa ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen kashe wani mai PoS, Abbas Yuguda, a karamar Hukumar Mayo-Belwa ta Jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Yahaya Nguroje, ya bayyana a wata sanarwa cewa Yuguda, yayin da yake dawowa daga sana’arsa, wasu gungun ‘yan fashi ne suka kai masa hari tare da raunata shi, suka bar shi cikin jini.
- Sallah: ’Yansanda Sun Yi Alƙawarin Tabbatar Da Tsaro A Kano
- Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Waya Masu Amfani Da Keke Napep A Adamawa
Nguroje ya kara da cewa, da samun labarin faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda suka ziyarci wurin, inda suka samu Yuguda a wannan hali, daga nan suka garzaya da shi wani asibiti mafi kusa, inda ya mutu a lokacin da yake karvar magani.
PPRO ya ce, “Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa ta kaddamar da bincike kan wani mummunan kisan da aka yi wa wani sana’ar POS, Abbas Yuguda, dan shekara 35, wanda aka kai wa hari a karamar Hukumar Mayo-Belwa.
“Al’amarin ya faru ne a ranar 22 ga Maris, 2025, a lokacin da wanda abin ya shafa ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya tashi daga wurin sana’arsa, wasu gungun mutane dauke da muggan makamai suka kai masa hari tare da yi masa munanan raunuka inda suka bar shi kwance cikin jini.
“Jami’an ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda, Mayo Belwa, sun isa wurin, inda nan take suka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibitin Cottage, Mayo-Belwa, domin kokarin ceton ransa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarsa a lokacin da ya ke karvar magani.”
Kakakin rundunar ‘yansandan ya ce, ya yi saurin shiga tsakanin wanda ake zargin da matasa suka kama shi domin cetonsa daga hannun matsan inda aka garzaya da shi asibiti.
Ya ci gaba da cewa wasu matasa a yankin da lamarin ya faru sun bi sawu inda suka kama daya daga cikin wadanda ake zargin ’yan fashi da makami ne kuma suka damke shi.
Ya gargadi mazauna jihar kan yin yin hukuncin nan na daukar doka a hannunsu tare da bukatar su da su kai rahoton duk wani abu da ya faru ga ‘yansanda.
“A bisa wannan karfi, daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Umar SNU, wasu fusatattun matasa ne suka bi sawun sa, inda suka yi ta kai ruwa rana kafin ‘yan sanda su kubutar da shi, sannan aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa, inda a yanzu ya taimaka wajen gudanar da bincike.
“Kwamishanan ‘yansanda, Dankombo Morris, ya yi Allah-wadai da wannan ta’addancin da kakkausar murya, sannan ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike don tabbatar da an gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kotu.
“Ya kuma gargadi jama’a da su daina daukar doka a hannunsu, ya kuma bukace su da su bar doka a kodayaushe ta yi aikinta, kuma su ci gaba da tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata, rundunar ‘yansandan ta bukaci mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan tare da kai rahoto ga ofishin ‘yansanda mafi kusa,” in ji Nguroje.
Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito a watan Disambar 2024 cewa wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari a unguwar Atan-Ota da ke karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar Ogun inda suka kashe wani jami’in tsaro da ke gadin wata karamar mota a yankin yayin da suka tsere da wata babbar mota da aka ajiye a dajin.
Wakilinmu ya samu labari daga wani mazaunin unguwar cewa wata mai sayar da abinci an gano gawarta a daji babu rai, inda aka yi masa fyade tare da daure ta a wata kusurwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp