Gagarumin aikin yaki da fatara ya fitar da wasu mutanen kasar Sin miliyan 98.99 daga zaman kangin talauci, ciki har da wasu sama da miliyan 9.6, wadanda suka samu zaman jin dadi ta hanyar sake tsugunar da su.
Zuriyoyin mazauna gabobin kogin Nu sun dade suna fuskantar matsalar zirga-zirga saboda manyan duwatsu.
Yau shekaru 4 da suka wuce, aka fara aikin sake tsugunar da mazauna wurin, abun da ya sa iyalin malam Luo dake kunshe da mutane 7 a kauyen Tuoping suka bar muhallansu marasa dadi dake cikin duwatsu, har suka cimma burinsu na samun galaba kan zaman talauci.
Ba gabobi biyu na kogin Nu kadai ba, a shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta kaddamar da gagarumin aikin sake tsugunar da mutanen dake zaune a wasu wuraren manyan duwatsu, ko wuraren dake fama da matsalar kwararar hamada da tsananin sanyi a tsakiya da yammacin kasar, a wani kokari na taimaka musu yaki da fatara.
An gina sabbin matsugunan mutanen da suka yi kaura kimanin dubu 35 a duk fadin kasar Sin, inda aka tsugunar da wasu sama da miliyan 9.6, al’amarin dake nufin cewa, an sake tsugunar da mutanen wata kasa mai matsakaicin yawan al’umma a duniya.
Mutanen dake fama da talauci zuriya bayan zuriya a kasar Sin, sun yi ban kwana da zaman rayuwarsu na da, har sun fara zaman jin dadi irin na zamani a wadannan shekaru 10 da suka gabata. (Murtala Zhang)