Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja a yau Laraba zuwa Paris, na ƙasar Faransa, domin ziyarar aiki ta makonni biyu.
A cewar mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu zai yi bitar mulkinsa na rabin wa’adi, inda zai tantance nasarorin da ya cimma da kuma irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa.
Sanarwar ta ce wannan lokaci zai ba shi damar tsara hanyoyin da za su inganta ci gaban ƙasa yayin da yake shirin cika shekaru biyu a kan mulki.
Duk da kasancewarsa a waje, Onanuga ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati tare da tuntuɓar manyan jami’ansa har zuwa lokacin da zai dawo gida.