Kungiyar Miyayyati Allah Kautal Gore ta maka gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom a gaban kotun kasa da kasa ta (ICC), bisa zarginsa da kwace wuraren yin kiwo guda 25,000 mallakar ‘ya’yan kungiyar.
Miyetti Allah ta bukaci kotun ta ICC da ta kawo dauki kan cigaba da tsare fulani makiyaya guda 4,000 da Gwamnatin jihar tayi, kan zargin cewa sun taka dokar haramta yin kiwo a fili da Gwamnatin jihar ta kafa.
Sakatare Janar na kungiyar ta kasa Saleh Alhassan ne ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai.
Alhassan ya ce, kungiyar ta Miyetti Allah ta kai karar gwamnan Ortom ne a gaban kotun ta ICC bisa kwace wa ‘ya’yan kungiyar wuraren yin kiwo a jihar har guda 25,000 sannan kuma ya bayar da umarnin garkame fulani makiyaya har 4,000.
A cewar Alhassan, Ortom na zuwa iyakokin da ke makwabtaka da Benuwai da Taraba ya na kwace shanun Fulani makiyaya inda hakan ke jefa rayuwar ‘ya’yan kungiyar a cikin halin kuncin rayuwa.