Hauwa Bala, matar marigayi Isah Bala, ɗaya daga cikin mafarautan da wasu gungun ’yan sa-kai suka kashe a yankin Uromi, da ke Jihar Edo, ta haihu bayan rasuwar mijinta.
Ta haifi yarinya mace ba da daɗewa ba, amma yanzu ta rage ita kaɗai ce wadda za ta ke jaririyar da sauran ‘ya’yanta guda shida, ba tare da wata hanyar samun kuɗin shiga ba.
- Sabbin Motocin Bas 100 Masu Aiki Da Lantarki Sun Fara Jigilar Fasinjoji A Birnin Addis Ababa
- Rundunar PLA Ta Kaddamar Da Atisaye A Yankunan Tsakiya Da Kudancin Zirin Taiwan
A cikin yanayi na kuka, Hauwa ta bayyana damuwarta game da halin da ta samu kanta bayan rasuwar mijinta.
“Ban san yadda zan kula da ‘ya’yana ba yanzu. Mijina ne yake ɗaukar nauyin komai,” in ji ta.
Marigayin Isah Bala ne ke ɗaukar nauyin duka buƙatun iyalinsa, har da kuɗin makarantar ‘ya’yansu.
Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta.
Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su.
Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar.
Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp