Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bayan zargin da ake yi cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi masa wasu alkawura masu tsoka.
Malam Shekarau, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance a wata wasika da shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta a zaman majalisar a ranar 29 ga watan Yuni.
Yayin da shugabannin NNPP suka samu labarin ficewar Malam Shekarau, sai tawagar mutum 3 da suka hada da dan takarar gwamnan jihar na NNPP, Abba Kabir Yusuf; dan takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila da kuma dan takarar majalisar wakilai, Kabiru Rurum, suka nemi ganawa da shi a daren Juma’a a Abuja, amma Malam Shekarau bai basu damar ganawa dashi ba.
Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa, Majiya mai tushe da ke da masaniya kan wannan shiri na sirri da Shekarau ke yi da kuma ganawar daban da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar; abokin takararsa Ifeanyi Okowa da; Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyochia Ayu, ta tabbatar da cewa tuni tsohon gwamnan ya “cimma yarjejeniya” da PDP kuma ana sa ran nan ba da dadewa ba zai bayyana ficewar sa a hukumance.
A cewar majiyar, a ranar Lahadin da ta gabata ma, Shekarau ɗin ya kira taron gaggawa na majalisar shura kan harkokin siyasa, tare da sanar da ƴan majalisar halin da ake ciki.