Tsohon gwamnan jihar Oyo kuma fitaccen masanin lissafi, Dr. Victor Omololu Olunloyo ya rasu.
Dr. Olunloyo ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi yana da shekaru 89 a duniya.
- Duk Da Matsin Tattalin Arziki, Bukukuwan Sallar Bana Ta Yi Armashi
- Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta
Marigayi gwamnan da aka haifa a ranar 14 ga Afrilu, 1935 zai cika shekaru 90 a cikin ‘yan kwanaki kadan.
Olunloyo ya jagoranci jihar Oyo tsakanin 1 ga Oktoba, 1983 zuwa 31 ga Disambar 1983.
Rasuwar marigayi dan siyasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon Editan jaridar Nigerian Tribune, Barista Oladapo Ogunwusi ya fitar a ranar Lahadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp