Ma’aikatar Hajj da Umrah ta Saudiyya ta bayyana cewa ranar 1 ga Dhul Qada (29 ga watan Afrilu, 2025) ce, ta ƙarshe ga duk wanda ya shiga ƙasar domin yin Umrah da zai iya zama.
Daga wannan rana, dole ne kowa ya fice daga ƙasar domin fara shirye-shiryen Hajji.
- Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
- Manufar Hade Aikin Raya Larduna Ita Ce Mabudin Kofar Cimma Zamanantarwa Da Samun Wadata
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta kuma ce ranar 15 ga Shawwal (13 ga watan Afrilu, 2025) ita ce ranar ƙarshe da za a daina barin mutane su shiga ƙasar domin yin Umrah.
Ma’aikatar ta ja hankalin dukkanin masu Umrah da kamfanonin da ke shirya tafiya da su tabbatar sun bi wannan doka.
Ta ce wanda ya karya dokar, wato ya wuce lokacin da aka ƙayyade, zai fuskanci hukunci.
Haka kuma, an gargaɗi kamfanonin da ke da alhakin kawo mutane Umrah cewa idan suka ƙi bayyana sunayen waɗanda suka ƙi dawowa gida, za a ci su tara har riyal 100,000.
Ma’aikatar ta buƙaci kowa ya bi doka domin guje wa hukunci.