Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Arsenal da Real Madrid za su kara yau Talata a filin wasa na Emirates a wasan kusa da na ƙarshe na gasar Zakarun Turai, bayan shekara 19 da suka wuce tun haɗuwarsu ta ƙarshe.
A baya-bayan nan, Arsenal ta lallasa PSV da ci 9-2 a wasannin zagaye biyu, yayin da Real Madrid ta doke Atletico Madrid ta samu shiga matakin.
- An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6
- Dole Dukkanin Masu Umrah Su Fice Daga Saudiyya Kafin 29 Ga Afrilu – Hukumomi
A tarihi, Arsenal da Real Madrid sun kara sau huɗu kacal, Arsenal ta yi nasara sau ɗaya, sauran ukun kuma sun tashi kunnen doki.
Real Madrid, wadda ta lashe gasar sau 15, na fatan doke Arsenal a karon farko, yayin da Arsenal ke ƙoƙarin lashe kofin Zakarun Turai karo na farko a tarihinta.
Ko Arsenal za ta ƙara doke Real Madrid, ko kuwa Real za ta kafa sabon tarihi?
Sai an ga yadda za ta kaya a Emirates yau.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp