Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Mannir Sanusi a matsayin sabon Galadiman Kano, ɗaya daga cikin manyan sarautun gargajiya a masarautar Kano.
Naɗin ya biyo bayan rasuwar Galadiman Kano na baya, Abbas Sanusi.
- Li Qiang Ya Tattauna Da Shugabar Kwamitin EU
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Satar Mota A Bauchi
Kafin wannan lokaci, Mannir Sanusi shi ne Hakimin Bichi, kuma ana yabonsa da shugabanci nagari.
Sauran sabbin naɗe-naɗen sun haɗa da:
- Turakin Kano ya zama Wamban Kano
- Adam Sanusi ya zama Tafidan Kano
- Ahmad Abbas ya zama Yariman Kano
Sarkin ya taya sabbin masu sarautun murna tare da jan hankalinsu da su yi aiki da gaskiya da kishin al’umma.