Masana kimiyya da masu masana’antu sun bayyana kafa dandalin musayar fasahohi da kirkire-kirkire ta hanyar hadin gwiwar Sin da Afrika, a matsayin mai muhimmanci wajen inganta tsare-tsaren samar da abinci da daidaita matsalolin yanayi da na kwari da cututtuka da raguwar sinadaran kasa.
Da suke jawabi a gefen taron makon kimiyya na rukunin tuntuba kan bincike a fannin aikin gona na kasa da kasa (CGIAR) dake gudana a Nairobin Kenya, mahalarta sun ce amfani da fasahohin rainon irrai, da yaki da kwari, da ban ruwa, za su taimakawa nahiyar shawo kan matsalar yunwa da ta nace mata.
- Kasar Sin Na Yaki Da Cin Zalin Da Amurka Ke Yi Ta Hanyar Dora Haraji Ne Bisa Sanin Ya Kamata
- Kasar Sin Za Ta Inganta Aminci Da Hadin Gwiwa A Asiya
Cibiyar CGIAR da abokan huldarta ne suka shirya taron na gefe mai taken “Gina Gadajoji” domin lalubo sabbin hanyoyin hadin gwiwa a bangaren aikin gona da kare mabanbantan halittu.
Manajan daraktan cibiyar CGIAR Ismahane Elouafi, ta jaddada cewa idan ana son rage tsadar shigar da abinci nahiyar, wanda a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 100 a kowacce shekara, zuba jari wajen inganta kyawun kasa da samar da ruwa da rainon ingantattun irrai masu samar da kyakkyawar yabanya, na da matukar amfani.
Ta ce nahiyar Afrika za ta iya cin gajiyar fasahohin aikin gona na kasar Sin, da wanda ya dace da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, domin bunkasa noma a cikin gida da ma fitar da amfanin gonar. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp