Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa abokiyar karawarta Borrusia Dortmund da ci 4-0 a filin wasa na Luis Companys dake birnin Barcelona a wasan zagayen na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai.
Barcelona ta kama hanyar lashe gasar inda ta ke kusa da tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe na gasar, kwallayen da Barcelona ta jefawa Dortmund babbar dama ce gareta na kaiwa matakin na kusa da na karshe.
- Yadda Kasashen Afirka Za Su Iya Rage Illar Harajin Amurka
- Amurka Ta Ƙara Wa Kayayyakin China Haraji Zuwa Kashi 104
Raphinda, Lewondowski da Lamine Yamal ne su ka ci wa Barcelona kwallayenta a wasan, duk da cewar Dortmund ta kai hare hare amma ta kasa huda ragar abokan karawar.
Idan Barcelona ta kai matakin gaba za ta hadu da PSG ko Aston Villa wadanda su ka buga dayan wasan da aka buga a daren ranar Laraba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp