Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Vietnam da su yi aiki tare, don wanzar da daidaito a tsarin ayyukan masana’antu da na rarraba hajoji tsakanin sassan duniya. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, ya yi kiran ne a jiya Litinin, yayin da yake zantawa da takwaransa na Vietnam To Lam a birnin Hanoi.
Ya ce Sin da Vietnam na rike da manufofin bude kofofinsu ga ketare, kuma sun jima suna taka rawar gani wajen wanzar da daidaito, da kawar da shingaye a tsarin ayyukan masana’antu da na rarraba hajoji tsakanin sassan shiyyarsu, tare da ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya.
- Sin Na Maraba Da Masu Zuba Jari Domin Su More Damammakin Bunkasarta
- Boko Haram Sun Kashe Mutum 300 A Sabbin Hare-hare 252 A Borno – Ndume
Shugaban na Sin ya kara da cewa, a matsayinsu na sassa da suka ci gajiyar dunkulewar tattalin arzikin duniya, dole ne Sin da Vietnam su karfafa muhimmiyar alkiblarsu, su hada hannu wajen nuna adawa da cin zali na bangare guda, da wanzar da daidaito a tsarin gudanar da cinikayya cikin ’yanci, da harkokin masana’antu, da tsarin rarraba hajoji tsakanin sassan duniya.
A nasa bangare kuwa, To Lam cewa ya yi Vietnam a shirye take ta yi aiki tukuru don kyautata tsare-tsare da hadin gwiwa da bangaren Sin ta yadda za a daga martabar cudanyar sassa daban daban, da nacewa ka’idoji 5 na zaman jituwa, da kare dokokin gudanar da cinikayya na kasa da kasa, da martaba yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin sassan biyu, da hada hannu wajen ba da gudummawa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp