Sanata Mohammad Ali Ndume, mai wakiltar kudancin jihar Borno a majalisar tarayya, ya bayyana cewa, kungiyar Boko Haram sun kashe kimanin mutane 300 a cikin sabbin hare-hare 252 wadanda mayakan Boko Haram suka aiwatar a watanni shida da suka gabata a fadin jihar.
Sanata Ndume ya kara da cewa, hakan ne ya sanya a kwanankin nan, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya jagoranci mukarraban gwamnati a jihar don neman daukin shugabannin sojoji kan lamarin.
- Amurka, Ki Fahimci Cewa “Girma Da Arziki Ke Sa A Ja Bajimin Sa Da Zaren Abawa”
- Mutane 2 Sun Rasu A Wajen Haƙar Ma’adinai A Jihar Neja
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema lalabai a ranar Lahadi, 13 ga watan Afrilun 2025 a Abuja.
“Ina daga cikin tawagar Gwamna Zulum wacce ta tattaunawa da Babban Hafsan Sojojin Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa tare da bangarorin shugabannin Sojan Sama, da na Ruwa a Abuja, inda shugabannin Sojin suka ce, Jami’ansu na iyakacin kokarinsu duk da karancin dakarun a fagen daga”. In ji Sanata Ndume.
A ‘yan kwanakin nan, kungiyar Ta’addanci ta Boko Haram ta sabunta hare-harenta akan sansanonin Soji da kuma kan al’umma da ke yankin Borno, inda tuni Gwamna Zulum ya nuna takaicinsa kan lamarin.
Saboda haka, Gwamna Zulum tare da Sanatoci Uku da wani dan majalisar wakilai, da ke wakiltar jihar suka yi taro da CDS, Hafsan Sojan Sama da Hafsan Sojan Ruwa domin tattauna batun sabbin hare-haren da Boko Haram suka kai musamman a jihar Borno.
“Muna cikin damuwa saboda tun daga watan Nuwamba na bara zuwa yanzu, mun sami hare-hare 252 a jihar Borno. A cikin wadannan lokutan na watanni shida, an kashe sojoji sama da 100. An kashe fararen hula sama da 200.” In ji Sanata Ndume.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp